Thursday 5 February 2026 - 15:47
An Bayyana Sakatare Janar na Hizbullah ta Lebanon A Matsayin Mataimakin Mahdi na Shekara

Hauza/ An bayyana Sheikh Na'im Qasim, Sakatare Janar na Hizbullah ta Lebanon, a matsayin Mataimakin Mahdi na Shekara na Babban Masallacin Jamkaran.

A wani rahoto daga Ofishin Yada Labaran Hauza, Hujjatul Islam wal-Muslimeen Sheikh Na'im Qasim, Sakataren Hizbullah ta Lebanon, saboda ayyukan sa na musamman a fannin yada tunani game da Mahdawiyya da kuma tsayawa tsayin daka a kan hanyar gwagwarmaya an zabe shi a matsayin Mataimakin Mahdi na Shekara na Babban Masallacin Jamkaran.

An yi wannan zaben ne sakamakon kokarin sa na ci gaba da goyon bayan wadanda ake zalunta, da fuskantar kungiyoyin masu girman kai, da kuma karfafa bangaren gaskiya.

Bikin bayyana mataimakin Mahdi na Shekara na Jamkaran ana gudanar da shi ne da nufin girmama manyan mutane masu tasiri a kan hanyar farfado da tunani game da Mahdawiyya da kuma al'adun jira (Intizar), kuma a wannan bikin ana karrama mutanen da suka taka rawa wajen bunkasa al'adar jiran mai ceto (Intizar) da kuma shirye-shiryen bayyanar Imam Mahdi.

A shekarun da suka gabata, an zabi wasu fitattun mutane daga kasashen Musulmi da dama a matsayin Mataimakan Mahdi, daga cikinsu akwai shahid Sayyid Hassan Nasrullah, Sheikh Ibrahim Zakzaky, Janar Haj Qassem Soleimani, shahid Abu Mahdi al-Muhandis, Ayatullah Sheikh Isa Qasim, janar shahidi mai rai Ali Fazli, da kuma Hujjatul Islam wal-Muslimeen Sayyid Hashem al-Haidari.

Lizimtar Waliyul Faqih na daga cikin Muhimman Alamu na Jira (Intizar) na Gaskiya

Huijjat Islam wal-Muslimeen Sheikh Na'im Qasim, Sakataren Janar na Hizbullah ta Lebanon, a jawabin da ya yi ta bidiyo a wajen bikin ranar tsakiyar watan Sha'aban (Nisfus-Sha'aban da kuma bikin karramawa ga "Maitamakin Mahdi na Shekara" na Babban Masallacin Jamkaran, ya jaddada muhimmancin Mahdawiyya wajen ceto mutuntaka, inda ya ce: Imam Mahdi (Ajtfs) shi ne fatan dukkan marasa galihu a duniya kuma alkawarin Allah na kafa adalci a fadin duniya.

Ya yi nuni da ayoyin Alkur'ani mai girma da kuma hadisai na Annabi, ya bayyana cewa: Duniyar yau tafi kowane lokaci bukatar jagorancin Imam Mahdi (Ajtfs), saboda duniya ta cika da zalunci, mulkin kama karya, da kuma girman kai, kuma hanyar tsira daya tilo ita ce cika alkawarin Allah na bayyanar Mai Ceto.

Sakataren Hizbullah ta Lebanon, yayin da yake bayyana cewa al'ummar Musulmi ya kamata su kasance a shirye kafin bayyanar sa, ya kara da cewa: Muminai ya kamata su kasance masu karfi, masu sadaukarwa, kuma masu gwagwarmaya, kuma shugabanni masu tsabta, masu gwarzantaka, da kuma su kasance masu sadaukarwa a fagen. Kuma wannan shi ne hanyar da a yau, ta hanyar alherin Allah, ake aiwatarwa a cikin al'ummar Musulmi.

Sheikh Na'im Qasim, yayin da yake ishara ga nasarar Juyin Juya Halin Musulunci na Iran, ya bayyana shi a matsayin wani ci gaba na musamman a kan hanyar jira (Intizar), inda ya ce: "Kafa Jamhuriyar Musulunci ta Iran a karkashin jagorancin Imam Khomeini (RA) a lokacin tashin hankali na duniya, wani babban mataki ne a kan hanyar shirye-shiryen bayyanar Imam, kuma a yau wannan hanya tana ci gaba da karfi a karkashin hikimar Jagora Mafi Girma, Hazrat Ayatullah al-Uzma Imam Khamenei (Dz)."

Ya jaddada cewa: "Jamhuriyar Musulunci ta Iran, ita ce gwamnatin Imam na Zamaninmu (Ajtfs), kuma tutar wannan juyin juya hali, a karshe za a mika ta ga hannayen Imam Mahdi (Ajtfs) masu albarka.
Sakataren Hizbullah ta Lebanon, yayin da yake ishara ga kafa kungiyar gwagwarmaya a Lebanon, Falasɗinu, da yankin, ya ce: Gwagwarmaya (muƙawama) ta samu asali ne ta hanyar jagorancin Imam Khomeini (RA) kuma a yau kowane mayakin gwagwarmaya yana kiran sunan Imam Mahdi (Ajtfs) kuma yana ganin kansa a matsayin sojan sa."

Sakataren Hizbullah ta Lebanon, yayin da yake tunawa da rawar da shahidai da kuma kwamandojin gwagwarmaya suka taka, ya bayyana cewa: "Shahidan muƙawama, ta hanyar sadaukar da rayukansu, sun nuna sadaukarwarsu ga Imamin Zamaninmu (Ajtfs), kuma jininsu yana shimfida hanya ga al'umma nuna ayarin bayyanar sa a matsayin na har abada.

Sheikh Na'im Qasim, yayin da yake bayyana cewa hanyar Imam Mahdi (Ajtfs) ita ce hanyar waliyanci, ya kara da cewa: "Lizimtar jagorancin Waliyyul Faqih, tsayawa tsayin daka wajen fuskantar mushrikai, Amurka, da kuma gwamnatin Sahayoniya, da kuma sadaukarwa a kan hanyar gwagwarmaya, na daga cikin mafi muhimman misalan jira na gaskiya da kuma gaggauta samun sauyi."

Ya yi ishara ga rawar da Masallacin Jamkaran ke takawa, inda ya bayyana wannan wuri mai alfarma a matsayin daya daga cikin wuraren da suka fi kusanci ga halartar ruhaniya ta Imamuz Zaman (AS), kuma ya jaddada ci gaba da halartar masu imani da addu'a a wannan wuri mai tsarki.

A karshe, Sakataren Hizbullah ta Lebanon ya yi godiya ga hukumomin Babban Masallacin Jamkaran saboda bayyana shi a matsayin «Mai Taimakon Mahdi na Shekara», kuma ya yi addu'a: "Allah Madaukakin Sarki ya gaggauta bayyanar Waliyyinsa, kuma ya sanya mu a cikin yaran sa, da mataimakansa, da kuma shahidai a karkashin tutar Imam Mahdi (Ajtfs)."

Tags

Your Comment

You are replying to: .
captcha